YANZU SHIRIN CIYAR DA MAKARANTU, NAIRA N100 KAN KOWANE KWANO

 

-Ma’aikatar Jin Kai Za Ta Gina Dakunan Girka abinci a Makarantu 60

Gwamnatin tarayya ta sake duba shirin ciyar da makarantun gida daga N70 zuwa N100 a kwanon kowane yaro.
Ministan kula da Harkokin jin kai Agaji da inganta rayuwar ‘yan najeriya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana haka a wajen taron tunawa da ranar ciyar da daliban Afirka karo na 7 da aka gudanar a Transcorp Hilton Abuja ranar Talata.
Sadiya Umar Farouq ta godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa wannan ƙarin da ya yi, inda ya ƙara da cewa hakan ya zo ne a daidai lokacin da kowa ya tashi tsaye wajen ganin an shigar da dukkan daliban makarantun firamare na gwamnati 1-3 cikin shirin.
“Zan so na yi amfani da wannan dama, wajen yaba wa mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amincewar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi a kwanan nan na sake duba farashin abinci na yau da kullum daga naira 70 zuwa 100 ga kowane yaro, wanda hakan ya zo tare da karuwar sa ido da tsauraran ka’idoji. Wannan ya zo ne a daidai lokacin da ake bukatar a tabbatar da cewa bamu bar ‘ya’yanmu a baya ba a harkokin ci gaba musamman ganin irin barnar da annobar COVID-19 ta haifar ga zaman lafiyar miliyoyin Al’umma a nan Najeriya.

“Hakan ne ma ya sa a shekarar 2020, a matsayin wani kokarin da gwamnati ke yi na dakile illar cutar, Ma’aikatar ta bayar da busasshen abinci ga gidajen da aka yi niyya a shirin a jihohin Legas da Ogun, da Abuja. Wannan ya yi dai-dai da manufarmu da aikinmu na tabbatar da cewa waɗanda ke cikin halin bukata anji koken su”.

Ministan ya kara bayyana cewa
An riga an tura jerin tsarin shirye-shiryen don haɓaka ingantaccen isar da shirin.

“A halin yanzu muna aiki kan tsarin shirye-shirye na shirin, sannan kuma za mu fitar da tsare-tsare masu inganci, tare da bullo da tsarin dafa abinci na Makarantu a kimanin misalin makarantu guda 60 a fadin kasar An ƙera waɗannan dakunan dafa abinci na Makarantu don su zama abin koyi, da kuma haɓaka cibiyoyin horar da masu dafa abinci tare da sauran masu amfana da shirin”.
Ministan ta kuma cewa ana kan shirye-shiryen samar da abinci kyauta ga yaran da ba su zuwa makaranta daga shirin NHGSFP, yayin da yake kaddamar da wani shirin na Alternate (ASP) nan ba da dadewa ba.

Ta godewa kungiyar abinci mai gina jiki ta Najeriya da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) saboda samar da tsarin sa ido da bin ka’idojin da ake bukata kan tsafta, amincin abinci da ingancin abinci. Har ila yau, ma’aikatar tana aiki kafaɗa da kafaɗa da shirin samar da abinci na duniya (WFP), wanda ke ba da tallafin fasaha, inganta iya aiki da kuma jagorar manufofin aiwatar da NHGSFP.

 

Tun a farkon jawabin, babban jami’in kula da harkokin zuba jari na kasa, Dr Umar Bindir ya bayyana cewa shirin ciyar da dalibai da aka bullo da shi a shekarar 2016 ya yi tasiri ga yara ‘yan makaranta ta hanyar samun karuwar yawan shiga makarantu da halarta da kuma inganta yanayin abinci mai gina jiki da lafiyar daliban da suka amfana.
A halin yanzu shirin yana da adadin yara miliyan 9,881,773 da suka yi rajista a sama da makarantu 53,000, wanda ya kawo zuwa yanzu an tantance dalibai miliyan 4.1 da kuma kama su a cikin Database na NHGSFP, a daidai lokacin da ma’aikatar ke ci gaba da ƙoƙarin samar da bayanan waɗanda suke cin gajiyar shirin a duk fadin kasar.
Sauran wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron tunawa da ranar ciyar da makarantun Afirka sun hada da babban jami’in gudanarwa na kasa kuma babban jami’i a sabuwar kungiyar bunkasa cigaban Afirka, NEPAD Nigeria Gimbiya Gloria Akobundu, Wakilin Gwamnan Jihar Nassarawa, Manajan Kula da Tsarin tsara Abinci na NEPAD Kefilwe Rhoba Moalisi da kuma sauran masu ruwa da tsaki.
Taken bikin ranar ciyar da makarantu na Afirka na bana shi ne ‘Ciyar da abinci da ci gaban jarin bil’adama a Afirka ta hanyar kara zuba jari a ciyar da yara a gida.

Saleh Farouq Gagarawa
(External Media Aid)
1-03-2022
Me rahoto wa

NNEKA IKEM ANIBEZE
(SA MEDIA)
01-03-2022

SADIYA UMAR FAROUQ TA KARBI LAMBAR YABO MINISTER JINSIYYA

An yi alkawarin ci gaba da tallafa wa mata domin su zama masu kawo canji acikin al’umma
Maigirma Minista mai kula da Harkokin jin kai Agaji da inganta rayuwar ‘yan najeriya Sadiya Umar Farouq ta samu karramawa ta DUSUSU lambar yabo na ministar jinsiyya na 2021.
A bikin da aka gudanar a hotel din Sheraton dake Abuja a ranar Talatar da ta gabata, Ministan ta godewa waɗanda suka shirya taron, DUSUSU Foundation (Dream Up, Speak Up, Stand Up) da suka bata babbar lambar yabo da aka yi wa Ministocin Jinsi, sannan ta yi alkawarin ci gaba da ɗaukaka mata domin su kawo canji a cikin al’umma.
“Kyautar lambar yabo na Ministar Jinsi da aka karramani dashi a farko ya bani mamaki, a matsayina Na Minista mai kula da Harkokin jin kai Agaji da inganta rayuwar ‘yan najeriya. Duk shirye-shiryen da ke ƙarƙashin ra’ayi na, mun yi ƙoƙari sosai don daidaita la’akari da jinsi tare da tabbatar da cewa an ba wa mata damar zama masu kawo canji a cikin yankunansu”.
“Aikina da na ma’aikatara sun fi mayar da hankali kan marasa galihu a Najeriya, a kowane yankuna, addini, kabila, Sanannen abu ne cewa waɗanda suka fi fama da wannan matsalar su ne mata da yara, kuma aikin mune mu karfafe su ta hanyoyi daban-daban”.
Ministar ta yi nuni da cewa, galibin waɗanda suka ci gajiyar tsarin shirye-shiryen da ma’aikatar ke yi, kamar su Shirin Canjin Kudi, Shirin Canjin Kudi na Matan Karkara, Shirin N-Power, Shirin Karfafa Kamfanonin Gwamnati da Shirin ciyar da Makarantu na Gida Mata ne, baya ga Shirin Madadin makarantu mai zuwa.
“Shirin Madadin Makarantu ya yi daidai da ka’idojin da DUSUSU ke yi na bayar da shawarwar inganta ilimi na duniya ga ‘yan mata a duk fadin duniya ta hanyoyi da dama harma da yadda zai amfane su”.
“Ina son mika godiyata a gareku da kuma kungiyar DUSUSU bisa jajircewar da kuka yi na kawo muhimman al’amura kan gaɓa, da tsayin daka wajen kawo sauyi mai cimma nasara”.
A nata jawabin, shugabar gidauniyar DUSUSU Zuriel Oduwole ta bayyana cewa an baiwa ministar lambar yabon ne saboda muhimmiyar rawar da take takawa a Najeriya da kuma gudunmawar da take bayarwa wajen ci gaban mata da ‘yan mata da kananan yara.
“Kyautar Ministan Jinsi ya biyo bayan tattara bayanai, tabbatar da abubuwan da suka faru, tattara bayanan waje, tabbatar da duk bayanan da aka karɓa, fayyace ma’anar samfurin da kuma tabbatar da tushen majiya daga ƙungiyoyin tallafi na waje daban-daban tun daga watan Yuni 2020 zuwa Yuli 2021”.
“Mun yi farin ciki matuka kan cewa tun lokacin da aka fara kyaututtukan shekaru 8 da suka gabata, wannan shine karo na farko kama daga turanci, faransanci, larabci, yaren Fotigal, da Mutanen Espanya, dama sauran su cewa mai karɓar wannan nau’in kyautar ya zarce ka’idoji ya kuma shiga aikin jin kai na jagoranci”.
“Ina taya wannan gagarumin canji mai ban mamaki, karo na farko a cikin mukamin minista na kasar wadda ta nuna cikakkiyar fahimta game da ayyukan jin kai da kuma bayar da goyon baya ga ilimin ‘ya’ya mata da kuma jin ƙan su a cikin sallamarta”.
A tun farkon jawabin, babban sakataren ma’aikatar Mista Bashir Nura Alkali, ya mika godiyarsa ga shugaba kuma wanda ta assasa lambar yabon na DUSUSU Zuriel Oduwole bisa karramawar da suka yi da kuma zabar ministan da akayi.
“Bayar da lambar yabo ta DUSUSU a yau wata shaida ce ta irin gagarumin ƙoƙarin da ta yi na ganin cewa an cimma burin shugaban ƙasa na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10 da suka wuce ta hanyar shigar mata cikin shirin sosai.”
Akwai sakon fatan alheri daga Karamin Ministan Ilimi, Mista Emeka Nwajiuba, Karamin Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Mariam Yalwaji Katagum, Barista Hanatu Munsawa, ma’aikatan ofishin Minista da ma’aikatar. Haka kuma akwai Daraktocin Ma’aikatar, abokai da masu fatan alheri.
NNEKA IKEM ANIBEZE
SA MEDIA
01-03-202

Gwamnatin tarayya ta assasa karin kasafi don cike gIBI a SHIRIN farfaɗo da wasu SASHEN da rikicE-RIKICE ke afkuwa.

Ministan kula da Al’amuran jin kai da sarrafa annoba da cigaban Al’umma, Sadiya Umar Farouq ta kaddamar da aikin farfado da yau a garin Abuja.
Shirin na (MCRP) a karkashin Hukumar Raya Arewa maso Gabas yana neman karin kuɗaɗe don ci gaba da tallafawa jihohin BAY (Borno, Adamawa da Yobe) ta hanyar bayar da agaji da kuma farfado da tattalin arzikin na dogon lokaci da nufin tallafawa Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Jihohin Arewa maso Gabas don samun gyara da inganta muhimman ababen more rayuwa da kuma isar da ingantaccen aiki na bunkasa rayuwa.
Yayin kaddamar da aikin, ministan ta bayyana farin cikin ta da sakamakon da hukumar (MCRP) ta samu, tare da yabawa kungiyoyin dake gudanar da aikin bisa kwazon da suka nuna tun lokacin da aka fara aikin.
“Za mu ci gaba da ba ku kwarin guiwa da ku kara himma, duk da cewa mun samu gagarumar nasara wajen farfado da ci gaban yankunan, akwai sauran ayyuka da dama da za’a yi. Wannan ya bayyana a cikin sabbin tsare-tsare na lambobin masu cin gajiyar shirin a cikin karin kudade na aikin da kuma shawarar da gwamnatin Najeriya da bankin duniya suka dauka na kara kudaden da kuma kara tsawon lokacin aikin.
Ƙarin kuɗaɗen aikin farfado da wasu sashe masu dimbin yawa wanɗan da rikice rikice ke yawan afkuwa, ya ba mu wata dama don ƙara ƙarfafa ci gaban da muka samu, tare da yin ƙarin aiki don tabbatar da cewa ’yan ƙasar da ke mabukata a faɗin jihohi ukun da aikin ya shafa za su iya dawo da rayuwarsu, samun ingantaccen kiwon lafiya. , ilimi, ruwa, tsaftar muhalli, tsafta da inganta hulda da zababbun jami’ai. Aikin yana nufin sauƙaƙe Ingantattun ayyuka ba kawai ta hanyar gina ingantattun ababen more rayuwa ba face tabbatar da haɓaka ingancin ayyukan da aka aiwatar wa.
“Tare da habaka assasa ƙarin kudin shiga kamar yadda aka gabatar a baya, fifikon inganta darajar aikin gona ya taka muhimmiyar rawa a cikin dabarun ciyar da yankin gaba bisa tafarkin ci gaba mai dorewa. Mun yi niyya a matsayinmu na gwamnati don samar da yanayin da jama’a za su amfana da dimbin filayen noma da ake amfani dasu ba don iya ciyar da kansu ba face har da ma jihohin da ke makwabtaka dasu”.
“Shigo da Najeriya a cikin ayyukan yankin na kasashen tafkin Chadi, wanɗanda ke makwabtaka damu; Kamaru, Nijar da Chadi, suna nuna mahimmancin musayar bayanai, tattaunawa akai-akai yayin da matsalolin sauyin yanayi, rashin aikin yi da rikice-rikice daban-daban suka mamaye iyakokinmu. Mafitar matsalolin da aka samo tare da kasashen dake da iyaka da Najeriya, za su ba da babbar dama don tasiri mai dorewa ga ƙasashenmu amma ga yankin tafkin Chadi. Za mu yi aiki kafada da kafada da kasashen dake makwabtaka damu domin nemo mafita mai dorewa kan ƙalubalen da muke fuskanta tare”.
Sauran wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron sun hada da manajan darakta na hukumar raya yankin arewa maso gabas Mohammed G. Alkali, wakilan bankin duniya, kungiyar tarayyar turai, USAID da Ofishin Harkokin Waje, (Foreign Commonwealth and Development Office) FCDO.

 

Gobara a Sansanin Yan Gudun Hijira a Borno:

Ministan Ma’aikatar kula da Al’amuran jin kai da sarrafa annoba da ci gaban al’umma, Ta jajantawa waɗanda gobarar ta shafa.
Maigirma Ministar ma’aikatar Al’amuran jin kai da sarrafa annoba da ci gaban Al’umma, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana bakin cikinta kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna El-Badawy, da ke Maiduguri a Jihar Borno.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da babban sakataren ma’aikatar, Bashir Nura Alkali ya fitar.
Ministar ta jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a gobarar.
A bayanin nata ministar ta kara da cewa, “Rahotannin da suka iso gare ni sun tabbatar da asarar rayuka, an kuma samu lalacewar matsugunai dubu uku (3,000).
Don haka Ministar tace, yawaitar barkewar gobara a Sansanonin ‘Yan gudun hijirar abin damuwa ne kuma Gwamnatin Tarayya da Hukumomin da abin ya shafa a Jihohin za su dauki matakan dakile afkuwar lamarin nan gaba.
A halin da ake ciki, Ministar tace “Na umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa da ta gaggauta aika kayan agaji ga wadanda abin ya shafa a sansanin, yayin da za a gudanar da tantance musabbabin gobarar da ma irin barnar da ta yi.
” Mai girma ministar tayi kira ga mutanen da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijiran da su yi taka-tsan-tsan don hana afkuwar barkewar gobara.

 

Parents of HAUWA still hopeful

In the climax of world’s outrage to the killing of a second aid worker, Hauwa Liman, by a faction of Boko Haram, her distraught family are still hopeful she is alive.

Hauwa, who works with the International Committee of the Red Cross (ICRC), was reported killed by the Islamic State West Africa Province (ISWAP), the second aid worker to be killed by the jihadists after Saifura Ahmed.

Her father Mohammed Liman says the heart-breaking news, barely a month after another aid worker – Saifura Ahmed – who was abducted with her in March was killed, is hard to believe.

“We feel so bad and we are in doubt if she is dead or alive because we didn’t expect her to be killed so suddenly,” Liman told Channels Television at the family home in Maiduguri, Borno State.

Liman, father of slain Hauwa

The family had expected that the insurgents would give the government time to meet their demands.

“In fact, we are in doubt because, unless we see her corpse or any evidence that shows she is dead, we still believe that she is living.

“She is living,” her father insisted with her mother and other women in the home breaking down in tears intermittently.

Struggling to keep his emotions in check, Liman appealed to the insurgents to understand that Hauwa was not a warring party and should not have been made to face the ordeal she faced.

“I appeal to the insurgents to release her because she is not a warring party. She is a humanitarian worker. She treats the young and the women and she is so helpful, even to them; not only to the whole society – even to them,” he said.

As many across the world struggle to make sense on the ever-more brutal approach adopted by the terrorists that have ravaged Nigeria’s northeast, Hauwa’s family wants the government to help them get closure.

“We appeal to the government, if she was dead at all, we want the corpse to be brought and we bury her. That will give us peace of mind. Otherwise, we will never forget such an incident in our lives,” her dad pleaded.

Iyakachi Liman weeps in reaction to the news that her daughter had been killed.

Hauwa’s mother, Iyakachi, like her dad, is struggling to make sense of the nightmare she has had to endure.

Despite repeatedly break in down in tears before speaking to Channels Television, she remains hopeful.

Speaking in Hausa, she explained that she did not expect that it would come to this.

“Up to this moment my mind has not told me that my daughter is dead. Because if you see what happened, these people want money. Now after Buhari agreed that he’d give the money, why is the gap between when he gave his consent and when this incidence happened so close?

“If a person wants money and they agreed to give him the money is he supposed to do this? Another thing is they (Hauwa and her colleagues) are humanitarian workers and are not supposed to be killed, and they are women.

Hauwa, the slain aid worker

“Why were they killed? And the ICRC had already pleaded with them to spare their staff and they even rendered them help as humanitarian workers. If this truly happened then it’s wrong. And, me, I strongly believe, that my daughter is not dead.”

“The government should investigate; if this girl is still alive, they should just bring her back. I don’t need anything except my child. If they can try and confirm that my daughter is well and alive, they should bring her back; that’s all,” she said.

Hauwa and two other aid workers – Alice Loksha and Saifura Ahmed Khorsa – were abducted by ISWAP on March 1, 2018.

While Hauwa and Saifura functioned as health workers with the ICRC, Alice worked with the United Nations Children Fund (UNICEF).

They were captured from Rann, a small town in Borno where thousands of internally displaced persons live in an IDP camp.

Abubakar Shekau, leader of a faction of and Boko Haram

The raid that led to their abduction was a bloody one with three other female aid workers and some soldiers killed.

Two of the aid workers killed in the attack were contractors with the International Organisation for Migration (IOM), working as coordinators in the camp believed to contain up to 55,000 IDPs who fled their homes because of the Boko Haram insurgency.

 

Must Read: TATA ya Fice Daga PDP da mabiyan sa

A yau ne Asabar Umaru Tata ya gudanar da babban taro a tsohon Gidan gwamnati na jihar Katsina.
Taron ya sami halartar Manyamanyan yan siyasa na jihar Katsina, ciki ya hada da Alhaji Sabo Musa Hassan, Mustapha Radda na jam’iyar PDP da Kumar Wanda ya bada masaukin taro wato Ibrahim Mu’azzam babban Darakta na yada manufofin gwamnan Katsina.
An gudanar da Muhimmin taron ne Dan fitcewar Umaru Tata da mabiyan sa daga jam’iyar PDP zuwa ga jam’iya Mai ci APC.
A fagen taron ne Umaru Tata yayi jawabi zuwa ga mabiyan sa inda yake cewa da dama ya fuskanci masaloli,wulakanci da cin mutum ci a jam’iyar PDP hakan yasa yaga lokaci yayi dazai bar PDP Dan shi ke Santa su suna kinsa. APC Kumar shi ke kinsu, su suna sansa.
Bayan jawabin Umaru Tata ne Alhaji Musa Sabo Hassan yayi maraba da zuwan Umaru Tata jam’iya mai ci wato APC, inda yake cewa shima da yayi PDP Kumar harda shi aka takurawa tata aka wulakantasa lokacin Shema, Alhaji Sabo daga bisani ya roki Tata ya yafe masa.
Bayan jawabin Alhaji Musa Sabo ne, Babban Daraktan yada manufofin gwamna yayi gaisuwar ban girma zuwaga Abdullahi Umar Tata, Ibrahim ya roki Mutane da su rungumi tafiyar Masari da zuciya daya, inda yayi kira ga Al’umar Tata da sauran su da suzo ayi tafiya tare, Ibrahim Mu’azzam ya Kara da karawa Mutane karfin guiwa na sana’ah.
Daga Karshe ne Abdullahi Umar Tata yace Rashin Zaman Sa gwamnan jihar Katsina bazai hana shi taimakon da yayi niyyar Yi ba karkashin gwamna masari inda yakara da cewa Duke masu yada manu fofin sa a yanar gizo toh su koma yada manu fofin gwamna Masari

Sickle cell community kick awareness program at Kano

Delirium as members of sickle cell community visits the secondary school at Kano state
On 2nd August 2018 Thursday, members of sickle cell community paid a visit to a secondary school at Kano state known as GSS Gwale.
The community gave a lecture on sickle cell and also offered students and teachers of the school free genotype test among which 5 teaches and 30 students were tested.
The program which was tagged SCC Awareness kicked off at exactly 11 am and lasted for about four hours students and teachers of the school also gained free counselling on SCD.
Among the entourage of the community were Dr, Aminu Abba, Dr Yusuf a haematologist at Aminu Kano teaching hospital and students of the medical lab of the said hospital.
However, the Executive members of the sickle cell community were headed by the Executive Director Shemau Adam Imam.
In a statement the public relation officer of the community Rukaiya Kamal said ” we felt there’s a need to go into schools especially secondary schools and create an awareness on sickle cell disease most importantly to encourage the students on premarital genotype test which we believe is very rare in our society and it’s the only possible way as at now we can break the sickle circle”
Teachers and students of GSS Gwale express satisfaction especially on the counselling and the genotype test of which the results were giving instantly, the head teacher of the school was also delighted and appreciated the kind gesture of sickle cell community.
By Saleh Faruq Gagarawa 
Airview News.

Jihar Kano ta yi rantsuwar kama da sabon mai magana da yawun Abdullahi Atta.

27 daga magoya bayan ‘yan majalisar dokoki 44 sun amince da yunkurin mai magana akai a wannan safiya.

Abdullahi Atta ne yake jagoranci a yau da sabon mai magana da yawun Alhassan Rurum a matsayin sabon mai magana da majalisar dokokin Jihar Kano.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce bai san abin da ya faru a gidan ba a yau.

Ganduje ya bayyana cewa bai san abin da ya faru a majalisar dokokin Jihar ba. Ya yi ikirarin sanar da shi ta hanyar kiran tarho ta magoya bayan jam’iyyarsa.

Ganduje ya bayyana cewa an sanar da shi cewa an gurfanar da wakilin majalisar dokokin jihar Abdul Atta.

Ya bayyana tarihin matsayin dimokra] iyya na gida, yana cewa irin wannan ci gaba na da kyau ga dimokuradiyya na ci gaba.

Gwamna ya bayyana hakan a gidan gwamnati.

Lokacin da sabon mashawarcin, hon Kabiru Alhassan Rurum da jami’ansa suka ba shi ziyara mai kyau.

“Ban san abin da ke gudana a majalisar jihar ba, wadanda manyan ‘yan gidan suka sanar da ni cewa’ yan gidanmu sun shafe shi.

“Kamar yadda ka sani, an samu kuma za su iya fassarar fassarar abin da ya faru, amma abu daya tabbatacce ne, wato, mu a Kano sunyi imani da dimokuradiyya na cikin gida.

Airview labarai